(ABNA24.com) Yayin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labaran Reuters a jiya Asabar Firayi ministan gwamnatin hadaka na kasar Sudan Abdallah Hamdok ya ce a halin da ake ciki, gwamnatin hadakar na bukatar taimakon dala biliyan takwas nan da shekaru biyu masu zuwa wanda hakan zai bata damar raya tattalin arzikin kasar wanda yake kan hanyar durkushewa sakamakon rikicin siyasa da kasar ta fuskanta.
Hamduk ya kara da cewa tuni ya fara tattaunawa da Asusun kasa da kuma Bankin Duniya domin ganin sun taimaka wa Sudan din da bashi.
A ranar Larabar da ta gabata ce aka nada Abdallah Hamdok a matsayin Firayi ministan gwamnatin hadakar kasar ta Sudan.
Tun a ranar 11 ga watan Afirilun da ya gabata ne Sojin kasar Sudan suka kifar da gwamnatin Shugaba Al-bashir, sannan kuma suka kafa Majalisar Sojin kasar wacce ta ci gaba da jagorantar kasar, inda bayan wasu kwanaki Majalisar ta shiga tattaunawa da kungiyoyin fararen hular da suka jagoranci zanga-zanga da kuma zaman dirshin wanda ya kai ga Sojojin suka kifar da gwamnatin Omar Al-bashir.
A makon da ya gabata, bangarorin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar karshe ta kafa gwamnatin hadaka wadda za ta jagoranci kasar nan da shekaru uku masu zuwa.
/129
26 Agusta 2019 - 08:59
Lambar labari: 971751
Firayi ministan gwamnatin hadaka ta kasar Sudan ya bukaci taimakon dala Biliyan 8 daga kasashen wajen domin raya tattalin arzikin kasar.